Labarai

INNALILLAHI: Sheikh Kabiru Ahmad Azare Ya Rasu

A ranar Alhamis Allah yayi wa Shahararren Mallam Sunnah Sheikh Kabiru Ahmad Azare (Jazi) rasuwa.

Sheikh ɗin ya rasu ne a babban asibitin gwamnatin tarayya na Federal Medical Center, Azare, (FMCA) bayan fama da jiyya da yayi tsawon watanni.

Kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar za gabatar masa da Sallar Jana’iza a gobe Juma’a da misalin karfe tara na safe (9:00am), a kofar gidansa da ke Anguwar Makarahuta a cikin garin Azare, ƙaramar hukumar Katagum da ke jihar Bauchi, Najeriya.

KARANTA WANNAN:  NIHORT Za Ta Binciko Sanadiyar Bullar Cutar Kankana A Bauchi

Ku sanya shi cikin addu’arku Allah Ta’ala madaukakin sarki ya gafarta masa da rahama, yasa hutuce agareshi, idan tamu tazo Allah Ta’ala yasa mu dace da kyakkyawan karshe.

Aamiin Thumma Aamiin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button